Buhari Zai tafi London domin a duba Lafiyarsa

0
73

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi zuwa birnin London a ranar 25 ga watan Yuni domin duba lafiyarsa.

Mista Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis a Abuja.

“Zai dawo Najeriya a cikin mako na 2 na watan Yuli”, inji sanarwar.

Kamfanin dillacin labarai na kasa ya rawaito cewa shugaban kasar ya dawo daga tafiyar da yayi ta baya zuwa London a watan Aprilu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here