Buhari Ya cika Alkawari ga Tsoffin ‘Yan Wasan Super Eagle na Shekarar 1994

0
69

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a bayar da gidaje masu dakuna 3 ga yan tawagar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle na shekarar 1994 wadanda suka samu nasarar lashe gasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika.

Gwamnatin tarayya dai a waccen lokacin tayi alkawarin bawa yan wasan gidaje bayan sun samu nasara a kasar Tunisia.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Garba Shehu ya yi bayanin cewar Sahalewar ta biyo bayan bukatar hakan da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde-Raji Fashola ya mika shugaban kasar.

Ya ce shugaban kasar ya amince da a abawa yan wasan gidajen a jihohinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here