A yau Laraba za mu Saki Sakamakon Jarrabawar UTME – JAMB

0
82

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB ta ce za ta saki sakamakon jarrabarwar UTME ta wannan shekarar a yau 23 ga watan Yuni.

Shugaban hukumar, Farfesa Is-haq Olayede, ne ya bayyana hakan a yau Laraba yayin taron manema labarai jihar Enugu.

Olayede ya ce ba shi da wani dalili da zai sa ya rike sakamakon jarrabawar.

“Yakamata ace an saki sakamakon zuwa yanzu, amma saboda bana babban ofis dinmu kuma bana son bada damar a saki a yayin da nake ziyarar aiki.

” Amma a yayin da na koma Abuja a yau za a saki dukkan sakamakon jarrabawar har wacce aka yi a yau saboda bamu da wani dalili na rike sakamakon jarrabawar”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here