Imam Mai Shekaru 20 Ya Lashe Zaɓen Shugaban Kungiyar Daliban Jami’ar Yusuf Maitama Sule

0
382

Muhammad Imam mai shekaru 20 ya samu nasarar zama shugaban kungiyar dalibai na Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano.

Imam wanda ke mataki na 3 a sashin ilimin Physics daga tsangayr ilimin kimiyya, an zabe shi a matsayin shugaban daliban jami’ar na 8 wanda kuma yake da karancin shekaru.

Kafin zaben nasa shi ne shugaban daliban tsangayar ilimin kimiyya na jami’ar.

An haifi Muhammad Imam a ranar 9 ga watan Agusta na shekarar 2000 a unguwar Diso dake karamar hukumar Gwale.

Ya fara karatun Firamare a makarantar Ma’aikata ta Kwalejin Fasaha ta Kano daga shekarar 2006 zuwa 2011, sannan ya halarci karamar Sakandire ta fasaha dake Kano daga nan ya ci gaba da babban Sakandire ta Governor’s College inda ya kammala a shekarar 2017.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here