Mutuwar Aure: Hukumar Hisbah ta Shawarci Ma’aurata su dinga Hakuri da Juna

0
152

 

Daga Maryam Sulaiman Maintain

Hukumar Hisbah ta jihar Kano tayi kira ga ma’aurata dasu zamto masu hakuri da juna domin rage yawaitar Mace-Macen aure a jihar.

Babban Kwamandan Hisbah Harun Ibn -Sina yayi kiran ne a ranar Alhamis data gabata yayin wani taron karawa juna sani, da akayi a Kano.

Kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN) ya rawaito cewa taken taron shine “Shawarwari kan zamantakewar aure da koma kiyaye yawan mace-macen aure.

A cewa shi, makasudin taron shine kira akan yawan matsalolin aure da Hukumar take samu a kullum, ya cigaba da cewa hukumar tana iyakar kokarin ta ganin an rage yawaitar sakin aure, da Kuma yadda ma’aurata zasu kaunaci junan su da fahimtar juna.

Yace, mafi yawan wanda ake saki yaran mata ne masu karancin shekeru masu yara hudu zuwa biyar hakan ya ka iya jawo musu matsalar kula bata garin kawaye.

Ibn-Sina ya kara dacewa yakamata duk ma’auratan da za suyi Sabon aure ya kasance an basu shawarwari game da aure, su shiga makarantu domin neman ilimin aure, sannan suje asibiti domin tabbatar da lafiyar su.

Kwamandan yayi kira ga iyaye da malamai su cigaba da kira da bawa Yaran su shawarwari kan aure.

A karshe Wazirin Kano, Alhaji Sa’adu shehu, yayi godiya ga hukumar akan taron, domin yana da yakinin aure da dama zai samu kariya sbd wannan taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here