Dan Wasan Kwallon Kafa Abdullahi Shehu Ya Auri Jaruma Murjanatu Yar Baba

0
523

Daga Junaidu Idris Gezawa

Shafin Kannywood celebrities ya wallafa labarin cewa, a yau ne aka daura auren Fitaccen Dan wasan kwallon kafa a arewacin Nijeriya, wato Abdullahi Shehu, da Amaryar sa wadda jarumar Finafinan Hausa ce mai suna Naja’atu Muhammad Suleman, wadda aka fi sani da “Murjanatu ‘yar Baba”.

An daura auren bayan an gama sallar Juma’a a garin Kano.

Naja’atu, ta fara fitowa a Finafinan Hausa, tun tana ‘yar shekara 10.

Kadan daga cikin Finafinan da fito sun hada da ” Murjanatu ‘Yar Baba, “Auren Gaja”, “Hakkin Rai”, “Harira” da sauran su kamar yadda shafin ya rawaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here