An Sanya Ladan Naira Miliyan 100 ga Duk Wanda ya gabatar da Nnamdi Kanu a gaban kotu

0
292

 

By Maryam Sulaiman Maintain

Gamayyar kungiyoyi 75 na arewancin kasar nan karkashin inuwar NCM ta bada sanarwar kyautar naira miliyan dari ga duk wanda ya kawo mata shugaban kungiyar inyamurai masu rajin kafa kasar Biafra Mazi Nnamdi Kanu domin ci gaba da shari’ar zargin sa da cin amanar kasa.

Kungiyoyin sun bayyana haka ne a Abuja a ranar Alhamis din da da ta gabata inda suka zargi Kanu hadi da cibiyar tsaro ta kudancin kasar nan da yin kalaman kyama da suka zamo silar harin baya-bayan nan da aka kai yankunan yan arewa mazauna yankin.

Mai magana da yawun kungiyar Dr Awwal Abdullahi Aliyu yayi kira ga kasar Amurka da Burtaniya da kuma kungiyar tarayyar turai da su dawo da NNamdi Kanu kasarsa ta haihuwa wato Najeriya domin girbar abinda ya shuka a gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here