Mun fitar da ‘yan Najeriya miliyan 10.5 daga talauci – Buhari

0
101

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, a jawabinsa na Ranar Dimokuraɗiyya, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce gwamnatinsa ta fitar da mutum miliyan goma da rabi daga ƙangin talauci cikin shekara biyu da suka wuce.

Ya ce: “Ƙudirinmu na cire ‘yan Najeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci cikin shekara 10 shi ne muradinmu duk da ɓarkewar annobar korona.

“Cikin shekara biyu da suka wuce, mun cire mutum miliyan 10.5 daga ƙangin talauci – manoma, ƙananan ‘yan kasuwa, masu sana’ar hannu, mata ‘yan kasuwa da ire-irensu.

“Ina da ƙwarin gwiwar cewa waɗannan miliyan 100 da muka sa a gaba za mu cimma su kuma hakan na nuna ci gaban da muka samu a ma’aunin rage talauci. Nan gaba kaɗan za a bayyana ƙarara tsarin da muka bi wajen cimma hakan.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here