Mazauna Ƙasar Saudiya Dubu 60 ne Kaɗai za su Gudanar da Aikin Hajjin Bana

0
150

Shafin Haramain Sharifain dake wallafa bayani kan aikin hajji a kasar Saudi Arabia ya bayyana cewa, Ma’aikatar kula da aikin Hajji da Umara ta kasar ta ce wadanda suke kasar Saudiya ne kadai za su gudanar da aikin hajji na shekarar 1442(2021).

A bayanin da shafin ya wallafa ya ce, maniyyata dubu 60 ne kadai za su gudanar da aikin hajjin na bana.

Maniyyatan da suka hada da yan asalin kasar da kuma yan kasashen waje mazauna Saudiya wadanda kuma aka yi musu rigakafin Korona na 1 ko na 2.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here