Matar da ta Haifi Ƴaƴa 10 Bayan Ɗaukar Cikin Wata 7 ta Kafa Tarihi

0
219

Wata mata yar kasar Afrika ta Kudu ta kafa tarihi a duniya yayin da rahotanni su ka tabbatar da cewa ta haifi ‘ya’ya 10.

 

Sithole mai shekaru 37, ta haifi ‘ya’ya maza bakwai da mata 3 ranar Litinin inda tayi fice kan matar nan yar kasar Mali, Halima Cisse wacce ta haifi ‘ya’ya 9.

A cewar rahotan, mijin Sithole ya tsammaci samun ‘ya’ya 8 sai dai matar tasa ta samu 10.

Mijin matar ya shaidawa jaridar Pretoria News cewa matar ta haifi ya’yan  cikin makwanni 29 da samun ciki.

“Ya’ya 7 ne maza da mata 3. Ta dau cikin watanni 7 da kwana 7. Ina farin ciki ina cikin nishadi bazan cika ku da surutu ba ku bari mun yi magana da safe”, inji Tsotetsi.

 

Ma’auratan dai suna da yan tagwaye guda biyu inda yanzu suke da ‘ya’ya 12.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here