Da kisan jama’a gara ɓallewar Biafra – Ƙungiyar Dattawan Arewa

0
120

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, Northern Elders Forum ta ce tana goyon bayan gwamnatin tarayya ta bai wa ƴan kabilar Igbo masu fafutukar kafa kasar Biafra damar ɓallewa cikin ruwan sanyi, maimakon kisan jama`a da ƴan IPOB ke yi babu gaira babu dalili.

Kakakin Kungiyar Dr Hakeem Baba Ahmed ta ce ɓangaren arewacin kasar ya san irin mawuyacin halin da ya shiga a lokacin yaƙin basasar da aka yi a baya, don haka yankin ba zai so a sake wani yaƙi ba.

“An yi yaƙi kowa ya ji jiki. Idan suna son su ɓalle kuma shugabanninsu sun goyi bayansu, ba wani dalilin yaƙi gara ma su balle domin ya fi zama alheri,” in ji shi

Ya ƙara da cewa babu wani shugaban Igbo da ya fito ya ce abin da suke yi na kashe-kashe da ƙone-ƙone su bari wanda ya nuna a cewarsa, “suna samun goyon bayan shugabanninsu.”

“Fitinar zamansu a Najeriya ta ishemu idan gwamnati ba za ta dauki mataki ba to ta ba su dama a yi ƙuri’ar jin ra’ayi .”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here