Mata Masu Zaman Kansu na son a Halasta Sana’ar Karuwanci a Afrika ta Kudu

0
104

Sashin Hausa na RFI ya wallafa labarin cewa,akalla Mata masu zaman kan su kusan 200 suka gudanar da zanga zangar lumana yau alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta kudu domin bukatar hukumomin kasar sun halarta sana’ar karuwanci da kuma daina kama masu irin wannan aiki suna hukunta su.

Wata daga cikin masu zanga zangar Dudu Dlamini sanye da ‘dan tofi da dogayen takalma ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar wadannan kaya ta ke sanyawa zuwa wurin sana’ar ta wadda ke bukatar kwarewa.

Dlamini ta ce karuwanci sana’a ce amma ba aikata laifi ba.

Constance Mathe da ta kwashe shekaru 16 ta na wannan sana’a ta ce a wannan sana’a ta yi nasarar sayen gida na kan ta.

Alkaluma sun ce akalla mata 120,000 zuwa 180,000 ke sana’ar karuwanci a kasar Afirka ta kudu.

Wasu daga cikin masu zanga zangar sun rufe fuskokin su, yayin da wasu kuma suka bar su a bude, a lokacin da suka samu rakiyar ‘yan Sanda.

Yonela Sinqu na kungiyar da ke kula da masu wannan sana’a ta ce ‘yan sanda na musu barazana wajen karbe musu kudi da kuma cin zarafin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here