Shugaban Ƙasar Turkiyya, Racep Tayyep Erdogon na Son Buhari ya goyi Bayan Falasɗinawa

0
204

Shugaban Kasar Turkiyya, Recep Tayyep Erdogon ya bayyana fatan cewa Najeriya za ta goyi bayan Falasdinawa a rikicin dake ake tsakanin Isra’ila da Gaza.

A wata wayar Salula da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban kasar ta Turkey ya ce sun tattauna muhimman batutuwa da shugaban na Najeriya.

“Mun tattauna da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Mun taya juna kammala Azumin watan Ramadan”, acewar Erdogon.

“Ina fatan cewa saboda kai hari kan Falasdinawa, kasashen duniya na yunkurin koya Isra’ila darasi kuma Najeriya za ta nuna goyan baya ga Falasdinawa.”

A ranar Asabar, fadar shugaban kasar Najeriya ta fitar da sanarwa inda ta ce Buhari ya tattauna da shugaban kasar ta Turkey ta wayar tarho.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya ambato Buhari na bayyana farin cikinsa da kyakykwar alakar dake tsakanin kasashen biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here