Kano Pillers ta Doke Adamawa United da ci 1 Mai ban Haushi

0
59

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta doke takwararta ta Adamawa United da ci 1-0 a wasan mako na 21 da suka kara ranar Lahadi.

Kano Pillars wadda ke buga wasanninta na gida a jihar Kaduna ta samu nasarar zura kwallo a ragar Adamawa United ne ta hannun dan wasa, Rabi’u Ali, kuma sauran minti 10 a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Pillars ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburi da maki 40 iri daya da na Akwa United wadda take ta daya, bayan da ta ci Dakkada 2-0 kamar yadda Sashin Hausa na BBC ya rawaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here