Kano: Duk Ɗalibin da bai Koma Makaranta a Gobe Litinin ba zai Fuskanci Hukunci – Kwamishina

0
183

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya yi kira ga iyaye da su tabbata ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci a yayin da aka tanadi hukunci ga duk wanda yaki komawa makarantar a ranar da aka sanya.

A sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Aliyu Yusuf ya fitar, kwamishinan ya ce dukkan daliban makarantun kwana za su koma makaranta yau Lahadi 16 ga watan Mayu, yayin da makarantun je ka ka dawo za su koma gobe Litinin.

Sannan ya yi bayanin cewa ma’aikatar ta kammala dukkan shirye-shirye don tabbatar da daliban sun dawo makaranta.

Hakan nan ya yi bayanin cewa gwamnati baza kyale dalibai su dawo makaranta a lokacin da suke bukata ba don haka akwai bukatar su bi doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here