Hukumar Kwastam Shiyyar Kano da Jigawa ta Tara Harajin Sama da Biliyan 7 a Watanni 3 na shekarar 2021

0
71

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa, shiyyar jihohin Kano da Jigawa ta tattara harajin Sama da Naira Biliyan 7 a farkon shekerar 2021 da muke ciki.

Kwantirolan Hukumar mai kula da shiyyar ta Kano da Jigawa, Sulaima Pai Umar ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin bayani kan yadda hukumar ta gudanar da ayyukanta tsakani watan Janairu zuwa watan Maris na wannan shekarar a shelkwatar hukumar dake Kano a yau Alhamis.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka yi fasa kwaurinsu

Ya ce idan aka kwatanta da shekarar 2020, inda aka samu Naira Biliyan 3, 898, 607. adadin ya ninku da kashi 100.

“Ci gaban da aka samu ya faru ne saboda jajircewar jami’ai da masu ruwa da tsaki wajen gudanar da ayyukansu”, inji shi.

Sannan ya yi bayanin cewa, hukumar hukumar ta kama kayayyakin da aka yi fasakwaurinsu zuwa kasarnan da suka hada da: Shinkafar yar kasar Waje, tsofaffin kayayyakin sawa, Taliya, Madara da Sabulu da Tayar mota wadanda dukkansu an hana shigo da su.

Hukumar ta ce duk da wayar da kai kan illar da fasakwaurin kayayyaki ke yiwa tattalin arzikin kasar nan amma wasu bata gari suna ci gaba da aikata hakan saboda san rai.

Haka kuma ya godewa, Hukumomin tsaro da masarautar Kano bisa goyan baya da suke ba wa hukumar wajen gudanar da ayyukanta.

Daga karshe ya yi kira ga yan jarida da su ci gaba da wayar da kan al’umma wajen yin biyayya ga manufofin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here