An Bayyana Sunayen Ƴan Canjin da aka kama a Kano Bisa Zargin Turawa Boko Haram Kuɗi

0
399

Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen mazauna Kano dake sana’ar canjin kudade wadanda ake zargin da turawa kungiyar Boko Haram kudade.

A watan da ya gabata ne dai mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Malam Garba Shehu ya yi zargin cewa wasu yan Najeriya na turo kudade ga kungiyar Boko Haram daga Kasar Dubai kuma suna aiki tare da yan canjin.

A cewar Jaridar Daily Trust, fitattun yan canjin da aka kama a jihar Kano sun hada da, Baba Usaini, Abubalar Yello(Amfani), Yusuf Ali Yusuf (Babangida) da Ibrahim Shani da Auwl Fagge da Muhamamd Lawan Sani(Mai Kawo Gwal).

Hudu daga cikin wadanda aka kama suna da alaka da mutane 2 da aka daure a Dubai shekarar da ta gabata kan irin wannan laifin.

Wadanda aka kama suna tsare a ofishin DSS da Soji a Abuja da sauran waurare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here