Sheikh Pantami Ya Barranta Kansa Da Kalaman Nuna Goyan Baya ga Ƙungiyoyin Ta’addanci

0
120

Ministan Sadarwa, Malam Ali Isa Pantami yayi karin haske kan wasu kalamai da yayi a shekarun baya kan kungiyoyin Al Qaeda da Taliban.

An ta sukar Ministan kan kalamana a shafukan Sadarwa wadanda wasu ke ganin na goyan bayan kungiyoyin ta’addanci ne.

Wasu masu amfani da shafukan sadarwa da masu sukar gwamnati sun nemi shugaba Buhari da ya sauke shi idan yaki barin kujerarsa.

Sai dai yayin da yake amsa tambayoyi a Tafsirin da yake gabatarwa na Azumi a Masallacin Annor dake Abuja yau Asabar, Ministan ya ce a yanzu ya gano abubuwa da dama kan kalaman da yayi a baya.

Ya ce sukar da ake yi masa a yanzu, tsagwaron siyasa ce kawai.

“Tsawon shekaru 15 ina zagayawa fadin kasarnan ina ilimantar da mutane kan hatsarin ta’addanci. Na je Katsina, Gombe da Barno da Kano da Diffa a jamuhuriyyar Nijar don yin wa’azi kan yaki da ta’addanci.

“Na tattauna da wadanda ke da akidun Boko Haram a wurare daban-daban. Na rubutu takardu a yaren Hausa da Turanci da Larabci. Na dawo da samari da dama kan hanya wadanda suka kaucewa hanya mai kyau.

” Wasu kalamai da nayi shekarun baya da ke haifar da ce-ce-ku-ce a yanzu na yi su ne bisa fahimtar lamarin Addini a wannan lokacin, kuma na sauya matsaya da na dauka a baya bisa samun sabbin hujjoji da kuma kara hankaltuwa.

“Ina dan karami lokaci da nayi wasu kalaman; ina jami’a yayin da nayi wasu kalaman ina karami. Na fara wa’azi tun ina dan shekara 13, malamai da dama da wasu mutanen basu fahimci wasu al’amuran dake faruwa a kasashen ketare ba shi yasa suke daukar matsaya kan wasu abubuwa bisa fahimtarsu, wasu suna sauya matsayarsu daga ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here