Idan kaga An Saki Mace Da Azumi to Laifinta ne -Salisu Abdul

0
243

Daga Salisu Abdul.

Da yawa za su yi mamakin jin cewa idan aka saki Mace da Azumi to Laifin tane, amma idan Mutum yayi la’akari da hujjojin da zamu bayar kuma ya dube su da idon basira babu shakka zai amince da wannan fahimtar tamu.

Da yawa Mata basa fahimtar sauyin rayuwa, su kurum ayi musu yadda aka saba yi musu, wasu gasu da hange, gasa da buri, da zarar sun ga wance Mijinta yayi mata kaza da kaza’to fa su ma haka zasu kwallafa rai sai su ma nasu Mijin yayi musu kamar yadda aka yiwa waccan, koda kuwa Mace ta san samun Mijin nata dana waccan ba daya bane. Wata haka zata yi ta hurawa Mijin ta wuta, shiga goma fita goma idan zai sai ta yi masa zancen, ga su da Mijin zai ce kiyi hakuri Allah ya hore sai ayi, wata ko to baza ta ce ba, bare tayi adduar Allah ya hore, kai wata ma tsaki kurum zata yi ta tashi.

Akwai rukunin Mata da idan suna da bukatar wani abu a wurin Mijin su ko suna so Miji ya siya musu ko ya basu wani abu to fa Mijin nan bashi da kwanciyar hankali har sai yayi musu yadda suke so ɗin. Irin wadannan Matan sune wadanda yayin da suka nemi Miji yayi musu wani abu ya kasa yu to fa su ma duk abinda suke yiwa Mijin sai su daina yi, wata sai kaga har gaba zata tsiri yi da Miji, ta daina kula shi, kawai don tace yayi mata kaza bai samu yayi ba. A irin wannan yanayin ne da Mazajen suke fita babu tabbacin zasu samu abinda suka fita nema, waje babu dadi, gida babu dadi, shine zaka ga Miji ba wuya ya dagawa Mace jan kati. Idan aka gamu da Namiji me zuciya a kusa yana ganin can ya fita bai samo ba, ya komo gida babu magana me dadi shi sai yaga kamar Matar ce ma ta hana shi ya samo, gashi ance Zomo baya fushi da Makashin sa sai maratayin sa ko kuma haushin kaza wuce kan dami, sai kaga ba wuya saki ya afku.

Akwai Matar da komai Mijin ta ya zo dashi bata san ta tare shi ta karba ba, kila ma bashi ya ciwo ya yiwo Cefane amma ya miko mata tace da fada baka san inda ake ajiyewa bane, ga bacin ran bashi ya ciwo ga haushin wadda yake ganin ya siyo domin ta bai ma ko burge ta ba, a nan ma sai kaga me afkuwa ta afku. Gashi mafiya yawan Mata kwata kwata su baiwa Mijin su hakuri baya cikin Ajandar su, wata akan ta yiwa Miji laifi tace yayi hakuri ta gwammace ya sake ta.

Mu kalli sakin Aure a lokacin Azumi, lokacin Azumi lokaci ne da bukatun gida suke karuwa gashi kuma an shiga wani yanayi sai dai addua, rashin godiyar Allah, da rainuwa da matsawa da Mace zata yiwa Miji na iya janyo mata saki nan take, musamman idan an gamu da Miji me saurin harzuka. Duk da haka akwai Mata masu hakurkurtar da Miji sa kwantar masa da hankali, tare da nuna masa kada ya damu don yau ya fita bai samo ba gobe sai yaga Allah ya bashi. Wallahi Mazaje masu irin wadannan Matan sun fi kulawa da gida domin zaka ga Allah Allah suke yi su samu su kai gida.

Amma dai Mata masu mita, rainuwa da rashin godiyar Allah sun fi yawa, kuma Maza ga matsalolin rayuwa sun yi yawa, don haka ya zama tilas Ma’aurata suke yin hakuri da juna, tare da kokarin zama tare ana tattauna matsalar gida da nufin warware ta tare, yawancin boyewa Iyali halin da ake ciki da kin fada musu gaskiya ko yi musu dungu shine ke janyo Mata basa yadda da babun Namiji. Allah yasa mu gane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here