Farashin Sukari na Kamfanin Dangote Bai tashi ba – Alhaji Sanbajo

0
126

Daga Rukaiyya Abdullahi Maida.

Hamshakin Dan kasuwa a jahar Kano Alhaji Salisu sanbajo ya ce farashin Sukari na kamfanin Dangote bai tashi ba.

Ya bayyana hakan ne, yayin ganawarsa da manema labarai a yau,inda ya tabbatar da farashin buhun sukarin har zuwa yau na Kan farashi Naira Dubu sha Takwas da Dari uku (N18,300).

Alhaji Sambajo ya Kara da cewa, wasu daga cikin Yan kasuwa ne ke son Yi wa kamfanin Dangote butulci, amma ko kusa kamfani bashi da alakar bisa Karin farashin sukari kamar yadda jita-jita ke yawo a cikin al’umma.

A karshe, Alhaji Sanbajo ya ce yawanci masu Karin kudin farashin sukari masu shagu na ne acikin unguwani inda ya ce farashin Bai sauya ba a cikin kasuwa tare da bayyanan irin kyakyawar Alakar da kamfani Dangote ke dashi wajen sausautawa al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here