Badaƙalar Filaye: A Shirye nake na Bada Shawarar Dakatar da Sarkin Kano Idan aka Same Shi da Laifi -Muhyi Magaji

0
389

Shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya kara tabbatar da cewa a shirye yake ya bada shawarar dakatar da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, idan aka same shi da hannu a badakalar filayen dake da alaka da masarautar Kano.

A wata tattaunawa da manema labarai Muhyi Magaji ya yi bayanin cewa hukumarsa ta samu wasu daga cikin mukkarabban fadar Sarkin da hannu a siyar da Filin Dorayi tare da karbar dalolin da suka kai kimar Naira 200, 000, 00.

Haka kuma ya yi bayanin cewa sun mika sammaci ga mukarabban fadar su 3 wadanda kamfanin da ya siyi filin ya bayyana sunansu.

Jami’an fadar sun hada da, Sarki Dan Rimi, Isa Pilot da Awaisu Abbas Sanusi, wanda shi ne Sakataren Fadar Sarkin.

Idan za’a iya tunawa dai, a yan kwanakin nan Muhyi Magaji ya fara binciken Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero bisa zargin siyar da Filaye a Gandun Sarki dake Dorayi Karama cikin birnin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here