Na Naɗa Mataimaka 55 Don Kakkaɓe Talauci -Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

0
127

Shugaban karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, Hassan Garban Kauye Farawa, ya nada masu bashi shawara da mataimaka 55.

Yayin da yake rantsar dasu, Farawa ya ce nadin nasu nada cikin dabbaka manufofin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na yaki da Talauci.

Ya bukaci wadanda aka nada din su gudanar da aikinsu yadda yakamata da sadaukarwa don ciyar da karamar hukumar gaba.

“Nadin mataimaka 55 an yi shi ne sakamakon kokarin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na kakkabe talauci tsakanin matasa da kuma bunkasa tattalin arzikin Kano a wannan lokacin”, Inji shi.

Shugaban karamar hukumar ya yi kira garesu su kasance jakadu nagari kuma su guji duk wani abu da zai bata sunan karamar hukumar Kumbatso da jihar Kano.

A kwanakin baya ma Kansilar Gurungawa a karamar hukumar Kumbotso ya nada mataimaka 18 lamarin da ya kawo ce-ce-ku-ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here