Kungiyar ƙwadago Reshen Jihar Kano ta Jingine Batun Tafiya Yajin Aiki a Yau Alhamis

0
215

Kungiyar ƙwadago reshen jihar Kano ta sanar da dakatar da tafiya yajin aiki da ta Kuduri aniyar Farawa daga gobe Alhamis.

Mataimakin shugaban kungiyar ƙwadago na ƙasa Usman Yaseen shi ne ya sanar da hakan a daren ranar Laraba yayin ganawar su da manema labarai.

Alhaji Usman Yassen ya kara da cewa Gwamnatin jihar kanon ta amince da biyan dukkan ma’aikatan albashin su da aka saba a baya daga watan hudu zuwa watan biyar kuma dole ce ta sanya faruwar hakan.

A Cikin wata takardar fahimtar juna da suka fitar na ƙunshe da sa hannun Shugabar ma’aikata ta jihar Kano, Kwamishinan Yaɗa labarai na Kano, da sauran su.

Wakiliyarmu Nusaiba Abdulaziz Muhammad ta rawaito mana cewa Sauran wadanda suka sanya hannu kan takardar sun haɗar da wakilai daga ɓangaren kungiyar ƙwadago matakin ƙasa da kuma shugaban kungiyar na jihar Comrade Kabiru Ado Munjibir.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here