Gwamnatin Tarayya ta Buƙaci Jihohi Su Dakatar da Bayar da Rigakafin Korona

0
245

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, Najeriya ta umarci jihohi 36 da babban birnin tarayya da su dakatar da bayar da allurar korona ta farko taAstraZeneca da zarar sun yi amfani da rabi daga cikin kasonsu da aka raba masu domin samun damar bayar da rigakafin ta biyu ga waɗanda aka yi wa ta farko.

Ministan lafiya Osagie Ehanire wanda ya bayar da umurnin ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da tabbas kan lokacin da za ta samu karin rigakafin bayan Indiya ta dakatar da fitar da dukkanin rigakafin da cibiyar Serum a ƙasar ke samarwa.

“Mun yi tunanin cewa ya fi dacewa a kammala yi wa waɗanda aka fara yi wa rigakafin gaba ɗaya,” in ji ministan.

A ranar 2 ga watan Maris ne Najeriya ta karɓi rigakafin korona kusan miliyan 4 na AstraZeneca.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here