Badaƙalar Filaye:”Muna Jiran mu ga ko Muhyi Magaji Zai Bada Shawarar Dakatar da Sarkin Kano” – Kabiru Dakata

0
288

Wata kungiya ta kalubalanci hallacin kasancewar Barista Muhyi Magaji Rimin Gado a shugabancin hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Kungiyar wacce ake kira “NASARAR GIDAN SARKI” ta yi bayanin cewa, a dokar da ta kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ma’aikacin gwamnati wanda ke da kima kuma wanda za’a iya amince masa, shi ne zai jagoranci hukumar. Wanda aikin majalisar dokoki ne ta tantance wanda zai shugabanci hukumar.

Kungiyar kuma ta nuna shakku kan cewa ko Muhyi ya taba aiki a matsayin ma’aikacin gwamnati, inda ta bukaci ya fadawa al’umma ma’aikatar da yayi aiki ya kammala.

“A lokacin da aka nada ka, shin ka bayyana gaban majalisar dokoki ta jihar Kano don tantancewa? Idan an tantance ka yaushe hakan ta faru?”, Inji shugaban kungiyar.

Kungiyar ta yi zargin cewa an karya dokar hukumar a nada Muhyi a matsayin shugaban hukumar.

Idan za’a iya tunawa dai, a yan kwanakin nan Muhyi Magaji ya fara binciken Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero kan zargin siyar da Filaye a Gandun Sarki dake Dorayi Karama a karamar hukumar Gwale.

Wani rahoton hukumar da Muhyi ke jagoranta, ya bayyana cewa, Sarkin na cikin badakar siyar da filayen, inda wani mai suna Yusuf Shu’aibu Aliyu ya siyar da Hecta 8 na fili a kan Naira Miliyan 575 da Hecta 14 kan Naira Miliyan 200.

Comrade Kabiru Dakata, wani dan gwagwarmaya a Kano, a wata tattaunawa da jaridar SAHELIAN TIMES, ya ce ” Muna jiran ganin ko Muhyi Magaji zai rubutawa Gwamna wasika tare da bada shawarar dakatar da Alhaji Aminu Ado Bayero”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here