Bayan Shafe Tsawon Lokaci a Rufe An Sake Bude Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano

0
152

A yau ne aka ci gaba da zirga zirgar jirage a filin sauka da tashin jiragen sama na malam Aminu Kano daga kasa zuwa kasa.

Wannan ya biyo bayan sanya ranar 5 ga watan Aprilu da gwamnatin tarayya tayi a matsayin ranar da za’a ci gaba da zirga zirgar jirage daga kasa zuwa kasa bayan dakatar dashi da akayi sakamakon annobar Korona.

Wakiliyarmu Nusaiba Abdul’azi Muhammad ta ziyarci filin sauka da tashin jirage na malam Aminu Kano domin ganin yadda aikace -aikace ke gudana a halin yanzu. Inda ta Bayyana mana Cewar an dauki matakan Kariya daga Kamuwa daga annobar Korona.

Kazalika wakiliyar tamu ta Samu ganawa da Mataimakin shugaban kwamitin dake yaki da Annobar Corona a jihar Kano Dr Sabitu shu’aibu Shanono wanda ya ce Gwamnatin jihar ta dauki sharadin da aka bayar tare da bin Ka’idojin da ya kamata Kafin Bude Filin,
Dr sabitu ya Kuma kara da Cewar daga cikin wasu matakan da Gwamnatin jihar ta dauki akwai Killace wadanda suka shigo jihar ta Kano daga wata kasar na Tsawon mako guda Kafin kafin ya tafi ga iyalansa,kana kuma da zarar an samu wani daga cikin wadanda suka shigo kasar bai matalan Kariya daga Corona Zasu dauki mataki akansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here