Gwamnan Bauchi Ya Samar da Madatsun Ruwa Kimanin 1120 a Jahar

0
217

Daga Maryam Sulaiman Maintain

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Gwamna Abdulkadir Muhammad kauran Bauchi ya kai ziyarar gani da ido na ayyukan da ya gada daga gwamnatin da ta gabata da kuma wadanda ya assasa a garuruwan Darazo, Dambam, katagum, Itas Gadau da kuma karamar hukumar Giade domin ganin yadda aikin ke gudana.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala rangadin, gwamnan ya ce gwamnatinsa zata tsaya tsayin daka don ganin an kammala ayyukan wadanda gwamnatin ta samu hadin guiwa da kamfanin African development partners, duk dai domin samar da ingantaccen ilimi a jihar.

Gwamnan ya ce sauran ayyukan da suka hada da samar da tsaftataccen ruwan sha na tafiya dai-dai a garuruwan Yelwa Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri, da Mashema, da kuma Itas Gadau.

Kazalika Gwamnan Bauchin ya ce an samar da Borehole 143 a karamar hukumar Dambam kadai, daga cikin guda dubu daya da dari da ashirin aka Samar a tsakanin jihar karkashin hukumar RUWASSA.

“ Nazo ne domin cigaba da zagayen aiki a shirye-shiryen da gwamnatin Jahar bauchi take yi domin sa ido da kan ingancin vayyukan. Na gamsu da mafi yawancen ayyukan sakamakon jajircewar masu aikin kamar yarda aka tsara.”

Ya ce “Mun Samar da ayyuka a bangaren kiwon lafiya, habaka ilimi, bijiro da hanyoyi, samar da ruwan sha mai tsafta, duk domin walwala da cigaban jahar.

Da ya ke rangadi asibitin Gabarin kuwa ya bayyana rashin gamsuwar sa da yadda aikin sabunta asibitin ke tafiya, in da yayi kira da masu ruwa da tsaki da su hanzarta Samar da kayayyakin zamani domin amfani ga marasa lafiya.

Ayyukan da Gwamna Bala muhammad ya kai ziyarar gani da idon sun hada da na sabunta makarantar model science Azare, Central Model School Mashema, Ginin karamin asibitin Wuro Nagge da ke Giade, sabunta karamin Asibitin Gabarin da kuma kammala karamin asibitin Kwankiyel.

Sauran sun hada da, gina framaren Maladu Ayuba a Dagaudan Dambam, asibitin sha ka tafi na Bulkachuwa, da kuma na karamar hukumar Azare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here