Fasahar Zamani: Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Tallafawa Matasa 250 a Kano

0
94

 

Tsohon Dan Majalisar Tarayya Me Wakiltar Kananan Hukumomin Kiru da Babeji kuma Babban Darakta a Hukumar Gidaje ta Kasa Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya tallafawa matasa 250 masu amfani da kafar sadarwa ta zamani akan fasahar zamani a mahaifarsa ta Kofa a Karamar Hukumar Bebeji a Kano.

Wadanda suka amfana da wannan tallafi sun fito ne daga Sanatoriya uku dake jihar Kano inda me girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da mataimakinsa da manyan jamian gwamnati suka halarta.

Tsohon Dan Majalisar kuma Jagoran Jamiyyar APC a yankin yace wannan tallafi yazo ne a lokacin da fasahar zamani take taka muhimmin rawa a shaanin tattalin arziki a wannan kasa.

Jibrin ya kara da cewa, makasudin wannan taro na tallafi shine a horar da wadanda suka amfana dasuyi amfani da wannan damar wajen sanin muhimmancin waya ga fasahar sadarwa da kuma alfanun ta ga harkar kasuwanci ta inda zasuyi amfani da damar wajen amfanawa kansu da yan uwansu domin samun rayuwa me kyau. Hakan zai basu dama wajen taimakawa gwamnati a kowanne mataki wajen yaqi da matsalar tsaro, cin hanci da rashawa da kuma wayar da kan alumma da sauran sakamakon da zai kara musu fahimtar abubuwan da karni na ashirin da daya yazo dasu.

A nashi bangaran, gwamna Ganduje ya nuna godiyar sa ga Hon. Jibrin inda ya umarci sauran yan jamiyya dasuyi koyi dashi..

An gabatar da takarda akan dabarun fasahar zamani wanda matashi kuma kwararre akan harkar Jappheth O Omojuwa ( Mawallafin littafin Digital: The New Code of Wealth) da kuma Ahmad Abdulkadir da sauransu suka gabatar.

Wadanda suka amfana da wannan tallafi kowannesu ya samu wayar zamani sabuwa, kudi da kuma kwafin littafin Jappheth O Omojuwa, littatafai da sauran takardu akan dabarun koyar da fasahar zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here