Mutane 7 Sun Mutu Bayan anyi musu Rigakafin Korona na AstraZeneca

0
155

Sashin Kula da lafiya na kasar Burtaniya a yau Asabar, ya ce mutane 7 cikin 30 dake fama da taruwar jini bayan anyi musu rigakafin Korona na AstraZeneca sun mutu.

Bayyana mutuwar mutanen da kasar Burtaniya ta yi na zuwa ne a yayin da kasashe da dama suka dakatar da amfani da rigakafin na AstraZeneca saboda sanya taruwar jini.

An samu rahotan samun cutar ta taruwar jini ta hanyar shafin yanar gizo na gwamnatin kasar bayan anyiwa yan kasar Miliyan 18.1 allurar.

Ba’a samu rahotan taruwar jini ba ga wadanda aka yiwa rigakafin Pfizer-BioNTech, a cewar sashin kula da lafiyar inda suka bayyana cewa suna ci gaba da bincike kan batun.

Damuwar da ake samu kan rigakafin ya sanya kasashe da dama dakatar da amfani da shi ko kuma takaita amfani dashi a iya dattijai.

Kasar Netherlands a ranar Juma’a ta dakatar da yin rigakafin na AstraZeneca ga mutanen dake kasa da shekara 60 bayan samun mutane 5 da cutar ta taruwar jini, sannan daya daga cikinsu ya mutu.

Kasar Jamus ma ta dakatar da amfani da rigakafin ga wadanda suke kasa da shekara 60 bayan samun mutane 31 da samun cutar ta taruwar jini.

Kasar Faransa ma ta yi irin wannan dakatarwar yayin da kasashen Denmark da Norway suka dakatar da amfani dashi gabadaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here