Ganduje Da Tsohon Sarkin Kano,Sanusi Sun Hadu a Kasar Nijar

0
468

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II sun samu damar haduwa a kasar Nijar a karon farko tun bayan da Gwamnan ya tsige Sanusi daga Sarautar Kano.

Tun bayan lamarin, ba a sake ganin mutanen biyun sun hadu a waje guda ba tun bayan da Ganduje ya tsige Sanusi.

Jaridar SAHELIAN TIMES ta rawaito cewa sabon shugaban kasar Nijar ne ya gayyaci Sanusi zuwa bikin rantsar da shi a yau Juma’a.

Haka kuma, Gwamna Ganduje na cikin tawagar gwamnatin tarayya a bikin rantsuwar.

Sauran wadanda ke tawagar gwamnatin ta tarayya sun hada da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da Aminu Waziru Tambuwal na jihar Sokoto.

Idan za’a iya tunawa dai, shekara guda da ta wuce, Ganduje ya tsige Sanusi tare da kirkiro sabbin masarautu guda 5 a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here