Gwamnan Jihar Zamfara na Shirin Ficewa Daga Jam’iyyar PDP zuwa APC

0
221

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kammala shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, an kammala shirye-shirye na sauyin shekar gwamnan, wanda shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC gwamna Mai Mala Buni zai gabatar da shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar wasu majiyoyi, an shirya komawar gwamnan zuwa APC ne yayin da tawagar gwamnatin tarayya ta ziyarci jihar Zamfara don jajantawa kan iftila’in gobara da ya faru a jihar.

 

Majiyoyin sun ce gwamnan ya shafe watanni yana tattaunawa da gwamnonin APC guda biyu.

Bayan gwamnonin biyu akwai kuma tsohon gwamnan jihar, Ahmed Sani Yerima dake ta kokarin ganin Matawalle ya dawo APC don rage karfin fada aji da tsohon gwamna Abdul’aziz yari yake da shi a jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here