Ahmed Musa, Shehu Abdullahi Sun Janyo cecekuce Sakamakon Sayan Kalandar SWAN Kan Dubu 50

0
128

Mambobin kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa(SWAN), reshen jihar Kano a yau Alhamis sun nuna al’ajabi yayin da fitattun yan wasan Najeriya, Ahmed Musa da Shehu Abdullahi suka sanar da farashi mafi karanci wajen siyan Kwafi na Kalandar kungiyar.

Lamarin ya faru ne yayin kaddamar da Kalandar kungiyar ta SWAN ta shekarar 2021 da aka yi a dakin Taro na cibiyar yan jaridu dake Kano.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Surajo Shuaibu Yahaya Janbul ya sanar da Siyan kwafi 10 kan Naira dubu 50 ga ko kowanne daya na yan wasan Biyu na Super Eagles.

Sanarwar ta sanya jama’ar dake wajen cikin mamaki ganin irin matsayin da yan wasan ke da su wadanda suka fara harkar kwalllon kafa a Kano.

A cewar wani daga cikin bakin da suka halarci taron wanda ya nemi a boye sunansa, ya ce bai kamata yan wasan bai dace su bada kalilan kudi kamar wannan ba kasancewar dukkaninsu suna buga wasa a kasashen keatare.

“Abin kunya ne kasancewar yan wasan nan basu halarci taron ba kuma an sanar da su. Abin takaici ne su bada yar wannan gudunmawar.

” Kar ka manta ita ce dai kungiyar wasanni ina magana kan SWAN wacce ta bude hanyar samun nasararsu a yau. Kowa zai yi tsammanin zasu fiye da abinda suka yi”, inji shi.

Wani shima wanda ya halarci taron ya yi bayanin cewa yan wasa bai kamata su bada irin wannan karamar gudunmawar ba kasancewar suna buga wasannni a kasashen duniya.

“Dubi yadda wasu wadanda ba shararru ba a fannin kwallon kafa suka siyi kwafi 5 kan Naira dubu 100”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here