Yau Laraba za a ci gaba da shari’ar Zakzaky da matarsa

0
55

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, yau Laraba za a ci gaba da shari’ar shugaban ƙungiyar mabiya Shia ta Islamic Movement in Nigeria (IMN), Sheikh Ibrahim Elzakzaky da matarsa Zeenat a Kaduna.

Zakzaky da matarsa na fuskantar tuhuma guda takwas da suka haɗa da kisan kai da taro ba bisa ƙa’ida ba da kuma takura wa al’umma da sauransu.

Sai dai shugaban da matarsa sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

Mai Shari’a Gideon Kurada na kotun Jihar Kaduna ya saka yau Laraba domin ci gaba da sauraron ƙarar ce ranar 8 ga watan Maris bayan lauya mai shigar da ƙara ya gabatar da shaidu guda 14.

An tsare Zakzaky da matarsa tun Disamban 2015 bayan rikici tsakanin mabiyan malamin da sojojin Najeriya, abin da ya jawo kisan ɗaruruwan ‘yan ƙungiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here