Abubuwan Sirri Biyar da Budurwa Ke Buƙata Daga Saurayinta Wanda Zai Kyautata Alaƙarsu

0
325

Fahimtar mata ya kan zama mai wahala a lokuta da dama idan baka sansu sosai ba. Sannan yana daga dalilin rashin fahimtar mata shi ne rashin samun isasshen lokaci na zama da su.

Akwai wasu abubuwa da mata ke so daga namiji amma baza su iya fada ma ba. Sai dai ka gane da kanka. Wadannan abubuwa su ne kamar haka:

1. Lokaci

Kowacce mace tana jin dadin lokacin da kake ba ta. Yan mata na son samari su shafe tsawon lokaci suna tare amma baza ta fadama tana so ba.

 

2. Gaskiya

Yin Biyayya babban al’amari ne da ke sanya budurwa mutuwar sonka. Yayin da namiji ke biyayya tare da fadin gaskiya ga budurwarsa, sonsa zai kara shiga ruhinta. Mace tana son namiji ya kasance ita kadai yake so.

3. So

Kowacce mace tana so a so ta. Idan mace taji baka sonta baza ta fada ma ba, sai dai ta fara nuna ma dabi’u na daban. Ba abinda mata suka fi bukata a alaka kamar soyayya.

4. Fahimta.

Yan mata na son samun fahimtar juna da samarinsu. Alakar ku za ta yaukaka ne idan kun fahimci juna.

5. Kudi

Babu wani mutun a wannan rayuwa da zai ce baya son kudi. Babban abinda budurwa take bukata daga saurayinta shi ne kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here