Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta Ayyana Juma’a da Litinin a matsayin Ranakun Hutu

0
168

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 2 ga watan Afrilu da Ranar Litinin 5 ga watan Afrilu a matsayin ranar Hutu don bikin ranar Easter na wannan shekarar.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da ranakun hutun cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Mohammed Manga.

Ya bukaci mabiya addinin kiristanci da su yi koyi da dabi’un jin kai, yafiya soyayya da hakuri gami da zaman lafiya wadanda Annabi Isah ya dabbaka.

Sannan ya yi kira a garesu da suyi amfani da bikin na bana wajen yin addu’ar zaman lafiya da hadin kan kasarnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here