Janar Sani Ya taya sabbin shugabannin Ƙungiyar tsofaffin Ɗalibai na Firamaren Shahuci Murna

0
121

Janar Sani ya taya sabbin shugabannin kugiyar tsofaffin dalibai ta Shahuci murna

Janar Ibrahim Sani ya taya sabbin zababbun shugabanni na kungiyar tsofaffin daliban firamare ta Shahuci murna.Ya yi kira gare su da su yi aiki tukuru don kare darajar firamare ta farko a Kano.

Janar Sani wanda shi ma tsohon dalibi ne a makarantar ya ja hankalin shugabannin karkashin jagorancin Barsta Dalha Daneji da su lura da muhimmacin makarantar wacce aka bude 1919 da iron rawar da ta taka a fannin ilmi a Kano da arewacin kasar nan.
Ya roke su su yi aiki tukuru don daukaka makarantar da ilmi.

Sababbin shugabannin sun hada da Amina Hassan mataimakiyar shugaba, Tijani Muhammad Yakasai Babban Sakatare, sai Khalid Imam mataimakin sakatare,inda kuma Nura Umar da Aminu Abdullahi suka zama sakatare kudi da maaji, yayin da Engineer Bello da Ambassador Nafiu Kofar ke jami’an hulda da jama’a na daya da na biyu.

Sauran sun hada da Anas Mai lemo jami’in walwala,Kabiru Yakubu matsayinOdita da Tijjani Muhammad mashawarci a fannin sharia.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here