2023: Gwamna Bala Muhammad ne Yafi Chanchanta Da Shugabancin Najeriya – Kungiya

0
165

Wata kungiyar Siyasa da tabbatar da ingantaccen shugabanci a Najeriya wacce ke goyan bayan Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ta ce Yan Najeriya basa amfana da hakkinsu dake kan gwamnati na tabbatar da tsaro da walwalar jama’a.

A wani taron manema labarai da kungiyar tayi ranar Lahadi a wajen kaddamar da shugabbanin reshen kungiyar na jihar Kano, Shugaban kungiyar Adnan Mukhtar Adam, ya bayyana cewa, gwamnan jihar Bauchi mai ci a yanzu, Bala Abdulkadir Mohammed(Kauran Bauchi) yana da nagartar da zai iya jan ragamar Najeriya a shekarar 2023, inda ya kara da cewa a yayin da babban zabe ke karatowa, a bayyana yake cewa abin da yan Najeriya ke bukata shi ne shugaban  da yasan aiki wanda zai kawo karshen matsalolin Najeriya.

A cewar Adnan, “A bayyana yake cewa Najeriya ba wai kawai an bar ta a baya wajen samun arzikin kasa da na al’umma ba wadanda suke a wadace sai dai matsalar wanda zasu tafikar da kasar, nagartattun shugabanni da zasu yi amfani da arzikin kasa don bunkasata. Bayanin haka yake kasarnan nada shirye-shirye da manufofi da zasu kai ta wani babban matsayi idan shugabanni sun aiwatar da su yadda yakamata.

“Haka kuma, abun bacin rai ne a yau duk da darajar da take da ita, kasarnan na fuskantar matsaloli masu tarin yawa da suka hada ayyukan yan bindiga, sace mutane da matsalar tattalin arziki gami da cin hanci da rashawa. Haduwar wadannan tarin matsaloli babu shakka sun kawo cikasa a ci gabanmu kasancewar ana fitar da kudade masu tarin yawa wajen dakile wadannan matsaloli”.

Kungiyar BAM-V ta yi bayanun cewa gwamna Bala Mohammed yana da nagartar shugabantar Najeriya bisa dubban dalilai da suka hada da yadda yake kishin kasa, inda a shekarar 2010 duk da kasancewarsa dan jam’iyyar ANPP ya ajiye siyasa a gefe don sanya muradin kasa a gaba yayin da ya gabatar da kuduri gaban majalisa wanda ya zama hanya ga mataimakin shugaban kasa a lokacin, Goodluck Ebels Jonathan ya zama mai rikon mukamin shugaban kasa a yayin rashin lafiyar Umaru Musa Yar’adu’a.

Sanann kungiyar ta ce, ” kokarinsa da himmarsa na yin maganin matsaloli da kalubale dake fuskantar kasarnan an gansu a lokacin da yake ministan Abuja.”

Kungiyar ta kuma bayyana cewa gwamna Bala Muhammad ne yafi chanchanta da zama shugaban Najeriya bisa gogewa da ayyukan ci gaba da ya gudanar a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya Abuja, sannan ta yi kira ga sauran yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da su goyi bayan takarar Sanata Bala Abdulkadir Mohammed don ci gaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here