Yanayin Hazo ya Kawo Cikas Ga Bikin Tunawa da Ranar Haihuwar Tinubu a Kano

0
247

Taron bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwar jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya samu tasgaro a yau Litinin sakamakon yanayin hazo da aka tashi da shi a Kano kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

A sakamakon hakan, da yawan manyan bakin da suka taso zuwa Kano wajen bikin an tilasta musu komawa da baya.

Manyan bakin da lamarin ya shafa sun hada da, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila; Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustaoha da Sauran Ministoci.

Mai magana da yawun, Osinbajo, Laolu Akande ya ce, Osinbajo zai halarci bikin ta kafar Internet tare da shugaban kasa Buhari.

Taron wanda aka tsara za’a fara shi da karfe 12 na rana, an dage shi zuwa 12:30 saboda rashin halartar manyan baki kamar yadda mai gabatarwa a shafin Zoom ya sanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here