Rashin Tsaro: Tinubu Na Son Gwamnatin Tarayya ta Ɗau Matasa Miliyan 50 Aikin Soja

0
245

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, a yau Litinin, ya shawarci gwamnatin tarayya ta dauki matasa Miliyan 50 aikin Soja don bunkasa yaki da ta’addanci, ayyukan yan bindiga da sauran abubuwan dake barazana ga tsaron kasarnan.

Tinubu na jawabi ne a taron bikin cikarsa shekaru 69 da ya gudana a Kano.

“A dauki Matasa miiliyan 50 aikin Soja”,inji shi.

Jagoran na APC yayin da yake mayar da martani kan kididdigar hukumar NBS na cewa yan Najeriya Miliyan 23 na fama da talauci, ya nemi gwamnatin tarayya ta samarwa da matasa aikin yi a fanni noma.

Ya ce, ” Kar ayi magana a kan jahilci, duk mutumin da zai iya rike bindiga, zai sarrafata ya yi harbi hakika zaj iya sarrafa motar noma a gona”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here