Kashe Miliyan Dubu 2 Wajen Sake Gina Duk Kilo Mita 1 na Titin Abuja Zuwa Kano Raina Hankalin Yan Najeriya ne -PDP

0
95

Babbar jam’iyyar Adawa ta PDP ta nemi gwamnatin tarayya ta sake yin duba bisa Kwangilar Sake gina titin Abuja zuwa Kano mai tsawon Kilo Mita 375 bayan bayyan cewa aikin zai lakume kudin da ya kai Naira Biliyan 797.23.

A sanarwar da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun Sakataren yada labaranta,Kola Ologbondiyan a yau Litinin Jam’iyyar ta nemi a gadunar da bincike a bude kan yadda aka kara yawan adadin kudin kwangilar daga Naira Biliyan 155 zuwa Naira Biliyan 797.

“Da amincewa da Naira Biliyan 797, ga titin da bai gaza Kilo Mita 375 ba, Gwamnatin Buhari na ikirarin gina duk kilo mita daya kan Naira Biliyan 2.12”, inji sanarwar.

 

Jam’iyyar ta nemi shugaban kasa Buhari ya gaggauta yin duba kan batun tare da mayar da Naira Biliyan 642 zuwa yin wani aikin.

 

Sanann ta nemi Buhari da ya kafa tare da bada dama ga hukumar EFCC da Majalisar Wakilai kan su gudanar da bincike kan batun kwangilar aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here