Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haram 49 a Jihar Barno

0
175

Sojojin Najeriya dake Runduna ta 28 a garin Chibok da Askira sun kashe yan ta’adda 48 tare da ceto mutane 11 da aka sace a jihar Barno.

Daraktan Yada labarai da hulda da jama’a na rundunar sojan, Mohammed Yerima ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Asabar a Abuja.

Yerima ya ce sojoji sun samu nasarar ne yayin da suka yi aiki da bayanan sirri na cewa masu tada kayar bayan na guduwa bayan hare-haren da sojoji ke kai musu a dajin Sambisa.

Ya ce Sojojin sun afkawa yan ta’addan a hanyar Chibok zuwa Damboa inda suka kashe 9 daga cikinsu yayin da wasu suka tsira da raunikan harbin bindiga.

Yerima ya ce, sojojin sun kuma kwace bindigar AK47 guda 7 tare da kubutar da mutane 3 da yan bindigar suka sace.

Haka kuma ya ce, sojojin dake Runduna ta 28 a garin Askira sun tarwatsa tawagar yan ta’adda a babbar hanyar Askira zuwa Chibok inda suka hallaka yan ta’addan 39.

Mai magana da yawun rundunar sojan ya bayyana cewa an kubutar da mutane 8 da mayakan Boko Haram din suka kama.

“Sai dai, daya daga cikin wadanda yan ta’addan suka sace yaji rauni a kafarsa a yayin da yake tsare a hannun wadanda suka sace shi.

” Tuni aka kai shi asibitin sojoji don kula da lafiyargsa”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here