Rahoto: Buhari ne Shugaban Ƙasa Mafi Talauci a Nahiyar Afirka

0
176

Mujjalar African Stand ta wallafa sunayen Shugabannin Afrika 10 da ta bayyana a matsayin wadanda suka fi Talauci a Nahiyar ta Afrika.

Ya zama kamar al’ada tsakanin jami’an gwamnati wajen amfani da ofisoshinsu domin tara dukiya da nufin Azurta kansu da yin rayuwar kasaita.

Zancen haka yake tun daga tushe, inda ake samun jami’an yan sanda na kasa-kasa zuwa manyansu dake yunkurin tara dukiyoyi.

A mukalar da mujallar ta wallafa ta bayyana sunayen shugabannin Afrika 10 da suka fi Talauci, kuma ta bayyana su a matsayin wadanda ke son barin tarihi bayan sun sauka daga karagar mulki.

Sai dai Mujallar ta bayyana Sunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban da yafi kowanne shugaba a Afrika Talauci.

Muhammadu Buhari ya zama shugaba mafi talauci a Afrika inda yake da adadin dukiyar da ta kai Dala dubu 150.

Jaridar Washington Post, a daya daga cikin rahotanninta ta bayyana cewa, Buhari shi ne shugaba daya a Afrika dake da karancin Dukiya. Rahotan ya ce Buhari shi ne mafi talauci idan aka kwatanta shi da sauran shugabannin Afrika.

Jaridar ta rawaito cewa, Muhammadu Buhari yana da gidaje 5 da gidan gona guda 2 a Garin Daura na Jihar Katsina, Sannan yana da shanu 270, Akuyoyi 25 da Dokuna 5 da gidan gona na kiwon kaji.

Rahotan ya bayyana cewa, Shugaban kasar ya samu wadandan kadarori ne ta hanyar da ba ta gwamnati ba. Sannan kuma bashi da Asusun ajiyar kudi a kasashen ketare bashi da kamfani ko rijiyar mai sai dai Buhari yana da hannun jari a Bakin UBA da na Skye.

Sannan Buhari yana da filaye guda biyu.

 

Sauran Shugabannin Afrika da jaridar ta wallafa sunayensu a matsayin matalauta sun hada da :

1.John Magufuli na na Tanzania mai karbar Albashin Dala dubu 4, 008 duk wata.

2. Sahle-Work Zewde ta kasar Ethiopia wacce ita ce mace ta farko a shugaban kasar kuma ta 3 a shugabannin matalauta a nahiyar Afrika.

3. Edgar Lungu na kasar Zambia.

 

4.João Manuel Gonacalves Lourenco na kasar Angola.

5. Evaristo do Espirito Santo Carvalho na kasar Sao Tome.

6. Adama Barrow na Kasar Gambia.

7. Pierre Nkurunziza na kasar Burundi.

 

8. Danny Faure na kasar Seychelles.

 

9. Idriss Deby na kasar Chad wanda ke da dukiyar da ta kai Dala Miliyan 50.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here