Matasan Arewa Sun Gargadi Ganduje Kan Shirya Taron Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Tinubu

0
183

Kungiyar matasan Arewa ta AYCF, ta gargadi gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano kan amfani da gidan gwamatin jihar a matsayin wajen shagalin bikin ranar haihuwar jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu.

Hakan ya biyo bayan zargin da ake yi cewa gwamnan na shirin amfani da gidan gwamnati a matsayin wajen taron.

A wata sanarwa da tafitar, Shugaban kungiyar ta AYCF, Alhaji Yerima Shettima, ya ce kungiyar bata ji dadin zabar gidan gwamnatin Kano a matsayin wajen da za’a gudanar da bikin ranar Haihuwar jagoran na APC ba.

Haka kuma, Kungiyar ta soki Tinubu bisa yin shiru da bakinsa yayin da aka kaiwa yan Arewacin Najeriya hari a wasu jihohin Kudu Maso Yamma.

Suka ce, “Yayin da aka kaiwa Yan Arewa Hari Tinubu ya yi shiru da bakinsa a yayin da aka lalata dukiyoyin yan Arewa a wasu bangarori na jihohin Arewa maso yamma”.

” Bai iya yin koda Allah Wadai ba. Amma duk da haka shi ne babban bakon Ganduje a gidan gwamnati.’

Sannan sun kara da cewa gwamnatin jihar Legas bata taba irin haka ga wani dan Siyasa a Arewa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here