Wata Takarda da Wata Mata ta ‘Saki Mijinta’ ta Jawo Ce-ce kuce a Shafukan Sadarwa

0
236

Wata takarda dake yawo a shafukan sadarwa na zamani ta haifar da ce-ce kuce a tsakanin ma’abota shafukan.

Takardar dai wacce ke dauke da bayanan da ke bayyana cewa wata mata mai suna Jummai ta Saki mijinta Mai Suna Ali Sani ta fara yawo ne a shafukan Sadarwa a Safiyar yau Alhamis.

Takardar wacce ba a tabbatar daga inda ta fito ba tana dauke da rubutu kamar haka:

“NI jummai Bala na Saki Mijina Ali Sani Saboda na Sameshi da lefin Yunkurin Neman Auren Kawata Mariya Idris.

“Hakan ya sabawa ka’idar da mukayi dashi kafin na Aureshi, Saboda haka ya bar min gidana, yaje auri Mariya da Uwarta Asabe da kakarta Talati da kuma Kakarta ta wajen Uba Uwani Mai Daddawa.”

Sai Dai Bayan Bayyanar Wasikar ne Samari da yan mata ke ta bayyana ra’ayoyinsu kan wasikar.

Yayin da wasu ke Raha da abin wasu kuma na ganin baikon mazan dake son Auren Jari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here