Matakai 6 da Zaka Bi Wajen Yin Rijistar Jarrabawar JAMB ta 2021

0
134

Hukumar Shirya jarrabawar shiga manyan Makarantu ta JAMB ta kaddamar da hanyoyin yin rijistar jarrabawar da za’a fara 8 ga watan Afrilu.

Ana saran za’a kammala rijistar a ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 2021.

Sannan za’a gudanar da jarrabawar gwaji ga daliban da suke da sha’awa a ranar 30 ga watan Afrilu.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, za’a gudanar da jarrabawar daga 5 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan.

Ga wasu matakai 6 da zaka bi wajen yin rijistar jarrabawar ta shekarar 2021.

1. Ka Samu Ka bude Email, hakan zai baka damar karbar duk wani bayani daga JAMB.

2. Kaje kayi Rijistar Katin dan kasa, JAMB ta ce dole masu son zana jarrabawar su mallaki katin dan kasa.

3. Ka ziyarci Shafin JAMB, ka kirkiri JAMB Profile.

Bayan kammala Rijista, zaka yi amfani da wannan Profile din ne don duba sakamakon jarrabawarka.

4. Ka duba Jamb iBass- yana da muhimmanci ka kula da wannan kafin kayi rijistar jarrabawar, kasan chanchantarka ta zana jarrabawar.

5. Siyan Jamb e-pin: Bayan ka tabbatar da chanchantarka sai kaje ka siyi Pin na Rijistar jarrabawar a Bankuna.

6. Bayan yin dukkan abubuwan dake sama, sai kaje cibiyar rijistar jarrabawar da bayananka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here