Ba Ɗan Siyasar Da Zai Tsaya Takara a Kano Sai Ya Nuna Shedar Fitar Da Zakka – Kwamiti

0
226

Darakta Janar na hukumar Zakka da Hubsi na Jihar Kano, Safiyanu Abubakar, ya ce ana shirin samar da tsarin tilastawa yan siyasa fitar da zakka kafin su tsaya takara a jihar.

Safiyanu Abubakar ya yi bayanin hakan ne a yau Alhamis a ofishinsa yayin kaddamar da kwamitin mutane 11 da za su dinga karbo zakka a jihar.

Acewarsa kokarin wani bangare ne na tallafawa mabukata a jihar.

“Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a kokarinsa na rage radadin da masu karamin karfi suke fuskanta, ya amince da nadinmu na jagorancin wannan kwamitin.

” Ya zama Wajibi ga dukkan mutane masu kudi da kamfanunuwa su bada wani kaso na dukiyoyinsu a matsayin Zakka”, inji shi.

Abubakar ya kara da cewa, hukumar ta zo da sabon tsarin karbar zakka wanda zai sa duk wani mai dukiya biyan Zakkarsa.

“Yan Majalisar dokokin jihar Kano, mussaman wadanda ke Kwamitin al’amuran Addini, sun zauna sun tattauna sun bamu damar karbar Zakka.

“A matsayin Kwamiti, muna kokarin samar da tsari wanda dukkan mai neman tsayawa takarar zabe a jihar dole ne ya nuna shedar biyan Zakka ga hukumar”, inji shi.

Tunda farko anasa jawabin, Shugaban hukumar, Sheikh Usman Yusuf, ya bayyana Zakka a matsayin daya daga cikin Shika-shikan Musulunci, inda ya ce ” Yayin da watan Azumi ke kusantowa akwai bukatar a bayar da ita ga mabukata a tallafa musu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here