2023: Zamu Ƙara Naɗa Sanusi a Matsayin Sarkin Kano tare da Rushe Sarakunan da Ganduje ya Ƙirkiro – Sabature

2
6911

Mai Magana da yawun tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin Jam’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusif(Abba Gida-Gida), Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa idan sun samu nasarar lashe zaben gwamna na shekarar 2023 cikin kwana 100 za su rushe gine-ginen da aka siyar ba bisa ka’ida ba.

 

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook inda ya ce zasu yi maganin “Wadanda suka lalata al’adu da kayan tarihi gami da tattalin Arziki”.

“Insha Allah, Kwanaki dari na farko zai kasance na rushe duk wani gini da aka yi a wajen al’umma.

“Sake Nada Sarki Sanusi tare da rushe Sarakun Kauye da mayar da Kano kasaitacciya Insha Allah”,  inji Sanusi Bature Dawakin Tofa.

2 COMMENTS

  1. Muna tare da Abba kabir Yusif Dari bisa Dari, insha Allah PDP kwankwasiyya zata karbi kano da Nigeria, dawowar Muhammad Sunusi ii kano alkairi ne agurin yan Arewa dama yan Nigeria gaba daya saboda haka muna fatan Allah ya nuna mana ranar dazai dawo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here