Yanzu-Yanzu: JAMB ta Fitar da Jadawalin Ranakun Zana Jarrabawar ta 2021

0
252

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta fitar da jadawalin zana jarrabawar ta wannan shekarar.

Hukumar ta ce, za’a zana jarrabawar ta UTME daga ranar Asabar 5 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan na Yuni.

Hukumar ta ce za’a fara rijistar zana jarrabawar daga ranar 8 ga watan Afrilu zuwa Asabar 15 ga watan Mayu, 2021.

Sannan ta ce baza ta kara wa’adin lokacin rijistar ba.

Hukumar ta bayyana hakan ne a sanarwar da shugaban sashin yada labarai na hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya fitar a yau Laraba.

Sanarwar ta ce hukumar ta dau matakin ne bayan taron da ta gudanar ranar 22 ga watan Maris.

Sanarwar ta kara da cewa dole masu son zana jarrabawar su sanya lambar su ta NIN kafin suyi rijistar jarrabawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here