Mun gamsu da yadda masu gidajen mai ke sayar da mai a Gombe -DPR

0
119

 

Daga Abubakar Rabilu, Gombe

Kwanturolan hukumar DPR a jihar Gombe Yerima Kollomi, ya bayyana gamsuwar su kan yadda masu gidajen mai suke sayar da man fetur a jihar ba tare da karkatar da shi ko tauye Lita ba.

Yerima Kollomi, ya bayyana hakan ne a lokacin da suka fita wani zagaye na bazata a wasu gidajen mai a jihar dan ganewa idanun su yadda ake sayar da mai din a jihar.

Yace suna sayarwa akan farashin da bai saba ka’ida ba Kuma babu wani gidan mai da aka samu da karkatar da mai din ko karya wata doka da za ta jawo a hukunta mai gidan mai ko a rufe gidan mai din.

Kollomi, ya kara da cewa Yan kura-kuran da aka samu da ba su Kai a rufe gidajen mai din ba an sa su sun gyara nan take Kuma sun ci gaba da sayar da mai din su.

A cewar sa matsalar da suka fi samu ita ce ta masu sayar da iskar gas da suke sayar wa a ko’ina akan hanya amma a kokarin da suke yi sun fara shawo kan lamarin

Daga nan sai ya hori masu gidajen mai din da masu sayar da gas na yin girkin da su tabbatar suna kiyaye doka domin idan suka Saba doka hukunci zai hau Kan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here