Da yiwuwar APC Baza ta Gudanar da Babban Taronta na Kasa a Watan Yuni Ba

0
144

Da yiwuwar babban taron jam’iyyar APC da aka tsara yi a watan Yuni, ba za’a gudanar da shi a watanba kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

Wani kusa a uwar jam’iyyar ta kasa ya tabbatar da hakan ga jaridar a jiya Litinin a Abuja.

Majiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa yayi bayanin cewa shugabbanin jam’iyyar a kowanne mataki suna sane sane da matakin, wanda za’a yi sanarwa a hukumance nan bada jimawa ba.

Idan za’a iya tunawa dai, kwamitin koli na jam’iyyar karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Disamba na shekarar 2020 ya amince da kara wa’adin wata shida ga kwamitin riko na jam’iyyar karkashin shugabancin Gwamna Mai-Mala Buni.

A watannin shidan kwamitin zai tsara sabun rijistar yan jam’iyyar, sulhu tsakanin mambobinta da zaben shugabannin kananan hukumomi da mazabu da jiha zuwa kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here